Wazobiya

Wazobiya

Adam A. Zango

Длительность: 5:34
Год: 2018
Скачать MP3

Текст песни

Wazobiya, rayuwa sai da naira
Babu naira, toh ko ka zam kwalele
Ehhh, yeh, yeh yeeeh

Eh ahayye sama ado kasa kudi yan matan duniya
Ayye sama ruwa kasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ehh, Allah bani kudi in sai gida in je aikin hajji (wazobiya)
Jama'armu ku saurara cikin kidanmu ba ma yaudara (wazobiya)
Kidan na bahaushe ne wakar ta Hausa ce kuma ba dabo (wazobiya)
Kalangu dan Hausa da ba'a yi mai jan kunnuwa (wazobiya)
Idan baku gane ba ina nufin bature nai nufi (wazobiya)
Don ko da ya ji zai jinjina wa Hausa da al'umma

Ehhh-hh-hh
Lai, lai, lale, lale kalangu shine kida

Ahayye sama ado kasa kudi yan matan duniya
Ahayye sama ruwa kasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ehh, Allah bani kudi in sai gida nayo aikin hajji (wazobiya)
Mata nayi kira gaba dayanku sai ku yi tarbiya (wazobiya)
Duk kyawun mace in babu kyan halin kyawun kawai (wazobiya)
Mata kuyi aure ku dena zagayawan bariki (wazobiya)
Toh ga wata tai kwantai saboda kun ga bata da tarbiyya (wazobiya)
Yawan tarnafiya yana ba mazaje sha'awa
Lai, lai, lale, lale kalangu shine kida

Ahayye sama ruwa kasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ehh, Allah bani kudi in sai gida in je aikin hajji (wazobiya)
Samari nayi kira a duniya ku bar yin yaudara (wazobiya)
Idan kunje tadi ku daina latsa yan mata haka (wazobiya)
In ko kun ki ji to in kuka haihu sai an maku (wazobiya)

Toh samari muyi sana'a mu daina dauke-dauke ga al'umma (wazobiya)
Toh duk nairar gaye idan da dan-hali nairar kawai (wazobiya)
Toh samari kuyi aure nai kira ku daina ruwan ido

Lai lai lale lale kalangu shine kida (eh, ah, ah, toh)

Ehh, Allah bani kudi in sai gida nayo aikin hajji (wazobiya)
Kai ka ji kidan naira da ko mahaukaci na rausaya (wazobiya)
Duk tsufan tsoho idan ya ganta sai yai rausaya (wazobiya)
Toh kogi ya kawo ku zo mu sanya gora muyi hito (wazobiya)

In dai naira ce da ka biye ta yanzu ka bata (wazobiya)
Naira mai sa fada da uwa da uba kai duniya (wazobiya)
In dai kana da naira gidanku kai ne alhaji (wazobiya)
Ko da kai laifi gidanku babu mai yi ma fada

Lai, lai, lale, lale kalangu shine kida

Lai, lai, lale, lale kalangu shine kida

Ehh, Allah bani kudi in sai gida in je aikin hajji (wazobiya)
Yaran zamani kuje ku yo karatu ya fi kyau (wazobiya)
Kai duk gayun gaye in babu ilimi hoto kawai (wazobiya)
Iliminmu na addini da boko ya zama garkuwa (wazobiya)

Toh mata kuyi ilimi domin ku bai wa ya'ya tarbiya (wazobiya)
Yarinya kyakykyawa ku zo ku ganta amma ba aji (wazobiya)
Ba arabi ba boko cikin gidansu ta zama akuya, meh (wazobiya)
Idan za'ai aure a dinga bincike kar ai tumun dare

Lai, lai, lale lale kalangu shine kida (aha)

Akwai wasu na magana da ni da Zango ba yan Hausa ba (wazobiya)
Kuce wacece ce kuce mai kace ta rage wa bakin ciki (wazobiya)
Idan kuma caca ta ci ta samu kurciya don suyi ciro (wazobiya)
Idan baka gane ba ka zo da Hausa zan ma tambaya (wazobiya)
Idan ka ban amsa in tarbatar bahaushe ne kake (wazobiya)

In dai a Hausa ne gidanmu babu baubawan bara (wazobiya)
Toh barewa ta yi burus cikin birgimarta a bariya (wazobiya)
Bar barna bara na kare wa ke bin mutum ba tarbiyya
Lai lai lale lale kalangu shine kida

Eh ahayye sama ado kasa kudi yan matan duniya
Ahayye sama ruwa kasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ahayye sama ado kasa kudi yan matan duniya
Ahayye sama ruwa kasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ahayye sama ado kasa kudi yan matan duniya
Ayye sama ruwa kasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Ahayye sama ado kasa kudi yan matan duniya
Ahayye sama ruwa kasa ruwa samarin duniya (wazobiya)

Yan matan duniya
Samarin duniya (wazobiya)

Yan matan duniya
Samarin duniya (wazobiya)

Yan matan duniya
Samarin duniya (wazobiya)

Yan matan duniya
Samarin duniya (wazobiya)

Yan matan duniya
Samarin duniya (wazobiya)

Duniya
Samarin duniya (wazobiya)

Duniya
Samarin duniya (wazobiya)