Nijar Ma Tamuce
Hamisu Breaker
3:51Da so yana rike amana ai bazai gujan ba Don na rike shi hanu biyu yanzu yayai min zanba Na kasa gane wanene ni akanki duba Kauna saka hawaye ne nata raunin gunba Na dauki agaran soyayya bazan gudu ba In so zakayi dan Allah zaka samu riba Idan na tashi bacci na ke nake tinawa Gani nake kawai kece zaki ban kulawa Bana tino dake zaki gujeni ban shiri ba Na daura damarar soyayyarki ban cire ba Hakan ya baki damar da kisani a ukuba Da damuwa cikin ruhinawa ban cire ba Basan abinda zai sanya yanzu ta fice ba In na rufe ido na hotonki ke nuna min Na kara angula sai nazari ya tabbatar min Idan na tina irin san da nai miki da me yayi min? Ina tana cikin ruhi haka yake tina min Yanzun nagane cewa so ne bazan kuma ba Shin me nai miki kika gwara kaina a jikin garu A lokacin da kika shaida jamma'a sun taru Kowa yanata kallona ni kuma ta faru Ga zuciya tana ta rayan cewa na kwaru Kaunarki tasaka ni naje samu miki faru Amma hakan ga bai sa kin mini adalci ba Idan na ganki kin damu hakan na damu na Sai inta tausayi naki ki zauna gefe na Na shaida haka nan sone na rike ki amana Koda baki tinowa ba haka bai damu na Don nai zama dake so bai sa na yinkure ba Mutan garin mu nai mini shewa suna ta cewa Wai so yanata dibana nayi haukacewa Na damu da rike soyayyar ki ban gazawa Idan na soki aganina nayi shalakewa Ashe roko na gani nazataki sai na duba Farin cikin masoyi ne ya samu mai bidar sa Idan ya samu mai sansa kuma cikar burinsa Ta zamto mallaki nasa hakan yasa a ransa Idan sukayi aure a ganin su babu kinsa Kawai su more shagalin su haka rai ya kunsa Domin sun sa a rai ba wani wanda zai raba Nasan akwai mutum daya wanda sukai mantawa Munafikin da shi kullum yaga an watsewa Shine burinsa rai nasa yaketa farantawa Ya manta zuciyar wasu ne yake yin batawa Nasan zaku tina soyayya na rushewa Amma silarta wanan ne in kai kirgawa Ga shawarata in yazo kar kuyi masa tarba Nasan da kin tino da abinda nake son cewa Amma koh kin tina ba amfanin ki rikewa A yanzu banda burin da kizo muyi zaunawa Nasan zakiyi hawaye wata ran kan ki macewa Domin kin cuci ruhina rabbi zai sakawa Ke kin saka hawaye igiya yana zubowa A lokacin na dauka da ni zanyi macewa Domin ina tinanin bake bazan iya ba Kurman dare makaho ai ni nake zamowa Idan dare yayi bacci nawa ban iyawa Sanan idan gari ya waye bana fitowa Amma akwai dalili daya wanda ke sakawa Na kara so cikin jamma'a har muyai gaisawa Wai me kike nufi san da kika ta fadan cewa Dani dake takalmin kaza babu cirewa Har alkawar kikai min wai zaki bani kulawa Ashe burin ki daman dake inyi amincewa Sanan sai ki sakamin rigar da ba cirewa Rigar farar kaya wanda ciki taka sokewa Amma ganin ido kyau a zubinta ba kushewa Ashe diyar macici na rike kamar zuma Yabon ta da nakeyi kullum babu irinta Don kwaliyyarta in nagani na karan santa Idan na kalla hanu nata koko kafafunta Sai in ga tayi zanen kunshi yabi jikin ta Hakan yake sakawa in ji nayo shaukanta Ashe zata kujen san da taso tasa a rai