Sakon Amarya
Hamisu Breaker
5:27Ya zanyi ne? Ya zanyi ne? Ya zanyi ne? Ance dare mahutar bawa Kwana nake ina yin kuka Cikin dare, yau gani da tsakar dare So shi kan bayyana cutar nan mai suna hawan jini Na kasance bani bacci cikin idanuna (idanuna) Sanadin soyayya da ta sauya duk tinanina (duk tinanina) Da ina ma mutuwa ta taho tazo ta dau raina (tazo ta dau raina) Zai fi min sauki na zama cikin dare fama Tun ina karami na so yayai tsuro a kirji na (kirji na) Na riga na saba kullum dani da mai sona (dani da mai sona) Koh zuwa makaranta sai ta biyo zuwa guna (zuwa guna) Gashi sai ni dai a cikin dare ina kerma Shekara ta haura ashirin da biyu mun girma (mun girma) So yana bunkasa ya ninka da a sau goma (da a sau goma) Zuciya na kin a bikin mu zamu yo hidima (zamu yo hidima) Ashe bazai yiyuba, Allahu shi yasan komai Wata ran na zauna a gida batai kirana ba (batai kirana ba) Zuciya na hangen laifi gare ta banyo ba (bazan yo ba) Sai waya tai ringing nai hanzari na duduba (na duduba) Chanken dake zuci itace take kira na ma Da na daga sai ko tace "ka taho kazo ka dauke ni" Ina cikin makaranta ka shigo kazo ka same ni (ka same ni) Na dauki mashin dina nai hanzari nace gani (nace gani) Kiran ajal a zama, a gida da ranta banzo ba Mun taho kan hanya tana ta bani labari (tana ta labari) Tana fadan yaya muje kadan, kadan kabar sauri (kadan kabar sauri) Sai wata babbar mota tazo ta doki bayan mu (doki bayan mu) Muka zube chan kas ta taka kanta mai sona Ina ta kuka kullum zuciya tana ta min kuna (tana ta min kuna) Sakin abin da yayi akwai abokanai guna (abokanai guna) Su suke lalashina nasani suna sona (nasani suna sona) Da babu su guna, kuka bazai tsaigaita ba Akwai Habib Director shima yana yi min jaje (yana yi min jaje) Ina da TK Adam shima yana yi min jaje (yana yi min jaje) Al'amin Dorayi AM nawa yayi min jaje (yana yi min jaje) Ina da SB Mamman shima yana ta min jaje Akwai Kamal Kanawa shima yana yi min jaje (yana ta min jaje) Ina da Hassan K Adam nawa yayi min jaje (yana yi min jaje) Ina da Abdul respect shima yana yi min jaje (yana ta min jaje) Kabiru Rudu, Auwal nawa sunyi min jaje