Share Hawaye
Hamisu Breaker
8:17Dawo Hamra yan mata Labarin kauna akwai dadi Wani sa'in so akwai daci Na zautu a kanki ba bacci So ya sanya ni lalaci Zuma ta zam mini madaci Hamra ki juyo sai naji dadi Labarin Hamra zan baku Hamra yan mata Wata ranar sallah ne hawan Ado Bayero na karshe In zaku tuna hawan Dorayi, hawan Ado yana yi Na fito ni da abokaina mu mu biyar a kyawun yanayi Kallon komawar sarki waigen da na dan yi Naga wani wal-wal haka hasken idanun Hamra ya janye ra'ayi na Su, su uku ne amma tinani na Hamra tazo gu na Zuciyata na raya min inje kusa inyi bayanin kaina Sai na dan juya nace wa abokina B Malik nai kamu Yace min me ka samo? Abdul respect ya dan yi murmushi ya dake ni yace abokina Wata yarinya a gefen ka naga kamar kalbin ta kwai kauna B Malik sai yace mu dan karasa muyi musu jawabi mana Ma'anar sa jawabin kauna Saina dan karasa nayo sallama a gareta ta amsa mini Sai nace "Baiwar Allah akwai gu nan ko a dan gusa mini" Sai tayo wani murmushi wanda duk yanayi na ya dadada mini Sai tace mini "Malam dan dakata haka karda ka takura mini" Amma ba komai don na sani soyayyace ta ja mini Sai nace mata "Kinga sunanki ne fa kawai zaki dan gaya mini" Umar Lastdon ya dan karaso sai yace mata "Kinga yan mata" Shi ya karasa duk jawaban da zan, shi ya furta mata manufa ta Mun yo nasara don mun yi sabo sosai ni da shi da ita Har Sarki ya wuce, mun wuce dukkanin mu muna ta bankwana Sai wata rana Mun dawo hanya Dan shaba sai ya tabo ni yace "abokina" Yaya sunan budurwar da kai ne, ko kuma a'a ba suna? Sai na dan yi shiru ina yin tunanin shin wai ta gayan suna Aiko bata fada min ba B Malik sai yace mu koma ai rai da rabo wata kila ma dace Aiko mun dace Na tambayi sunanta sai tace min wai sunanta ita data Sai ta nuna min kawarta tace min wannan kuma wai goba Dayar data karaso tace dani "Ni kuma sunana yalo" To kai yaya sunan ka? Sai nace "Suna na Hamisu Breaker Dorayi, haka suna na" Sai Hamra ta karaso tace dani "Sunana na gaskiya Hamra" Eh kwarai Hamra Sai na ce. "A ina kike?" Ta ce, dani "Nassarawa" a nan ne ta zauna Kawarta ta ce. dani "A'a mu a Kaduna nuka yiwo zaunawa Ba 'yan Kano ne ba Suka ban lambar waya wadda zana kira su mu dinga gaisawa Mun fara waya da su haka mai dadi sun deben kewa Daga baya idan na kira su sai inji layin yayi yankewa Layin anyi kullewa Wayyo Allah na Hamra (dawo Hamra yan mata) Na daina ganin ki Hamra (dawo Hamra yan mata) Ban jin muryar ki Hamra (dawo Hamra yan mata) Yaya zanyi na ganki Hamra