Lokaci
Hamisu Breaker
5:16An daura auren kauna Ni Breaker waka Rana na kowa murna Share hawaye Amarya share hawaye Aure bautar Allah ne Amarya share hawaye (share hawaye) Aure bautar Allah ne Ya amarya share hawaye (share hawaye) Aure bautar Allah ne (bautar Allah ne) Farko nasa sarki na (amarya) Sarkin da yayai ummi na (amarya) Da wanda yayai abba na (amarya) Abin nufa da bukata, bani damar waka Amarya share hawaye (amarya, amarya ta ango) Aure bautar Allah ne (amarya, amarya ta ango) Ni Breaker waka Ya rabbi kara salati (amarya) Da ba sakan ba minti (amarya) Ga daha nurizzati (amarya) Kasa da kaf ahalinsa Har sahabai kasaka Amarya share hawaye (share hawaye) Aure bautar Allah ne Share hawaye Ke amarya daure, daure (amarya) Kuka kibar hawaye share (amarya) Yau gidanki zaki kitare (amarya) Sai ki kwana dakin 'yanci Daina kuka daure Amarya share hawaye (share hawaye) Aure bautar Allah ne Kinga kinyi nasara duba (amarya) Tagari ya ji ni Amarya share hawaye (share hawaye) Aure bautar Allah ne Ni Breaker waka Kinga aure shi sunna ne (amarya) Sanan kinsan aikin lada ne (amarya) Kinga ke yake kauna ne (amarya) Hakan yasa ya nemi ki yarje Kuyi zama na amana Amarya share hawaye (share hawaye) Aure bautar Allah ne Hamisu Breaker mai waka ne (amarya) Nazo murnar biki nataya ne (amarya) Bude ido amarya ki gane (amarya) A gun bikin aurenki Ni nake miki waka Amarya share hawaye (share hawaye) Aure bautar Allah ne Toh ango gareka na dawo (amarya) Wata yar shawara ce na kawo (amarya) Idan an kai ta to ba yawo (amarya) Tattalinta sai karika duk Ta zamo matarka Amarya share hawaye (share hawaye) Aure bautar Allah ne (bautar Allah ne) Iyayen mu gani gareku (amarya) Jinjina ta girma gun ku (amarya) Kunga kunyi auren 'yarku (amarya) Lafiya kalau da lumana A gidanta ta zauna Amarya share hawaye (share hawaye) Aure bautar Allah ne Amarya, amarya ta ango Ya amarya, amarya ta ango Aunty a dole in gaishe ku (amarya) Dan gareku bani da shakku (amarya) Mai waka dole in gaishe ku (amarya) Naga kwalliya da zubin ku Kunyi babbar harka Amarya share hawaye (share hawaye) Aure bautar Allah ne (bautar Allah ne) Kawayen amarya na gaishe ku (amarya) Kuma ga jinjina ta girma a gareku (amarya) Zana roki alfarmar ku (amarya) Idan kun kai amarya daki Sai ku barta da ango To ni anan nake bankwana (amarya) Nasan dani daku kwai kauna (amarya) Kara gareni yau kun nuna (amarya) Ba abinda zan ce ni sai Godiya ga masoya Amarya share hawaye (share hawaye) Aure bautar Allah ne Share hawaye Bautar Allah ne