Sha Awanatu
Hamisu Breaker
4:03Idan kaji kugi kasani akwai labari Bayanin gaskiya wanda ba ayin kari Labarin mai sona da gaske zanyi a tsari Wanda ya sanni da ita ya sanni dan mun saba Akwai so a cikin zuci wanda bashi da riba Kaso wanda yake san wani ba kai dace ba Amman ni soyayyar da nayi banyi kure ba Ina so ta ta so ni sanda banyi zato ba Kafin na kai ku da nisa Dorayi dama nake Unguwar Bello a nan nake sana'ar dinki A inda nake kuma gidansu ma a layin yake Gani na farkon ta da nayi zuciya ta harba Shekaru matsakaita kaunar mu tayo girma Gini mukeyi tare gidansu an sallama Tazo da safe da yamma dare gidansu na koma Kina birge kowa masoya dukka sun yaba Akwan' a atashi Muna kara shakuwa mai tsanani Tana yin wanka tayi kwaliya duk dan ni Kuma tayo kunshi tai flower duk dan ni ne Idan tazo nunan bani nan baza ta tsaya ba Masoyiya ta na tare yan kudin ta tabani Tana yi mini hidima abinda zanyi tayi min Toh matsalar farko ba kudi na aure gare ni Gashi ta girma a lokacin da ban aune ba Gidan su ance, "Na fito idan da gaskiya nake" Kuma ni santa a zuci na riga na rike Idan aka fadan in barta kuma kuka nake Rai na ya bace ayi fada dani koh da ba a so ba Lallai akwai al'ajabi a so na gaskiya Da kaina nai mata maganar da zata waiwaya Na ce, "Tayo aure zai fi mata gaskiya" Ta ce dani, "Na bari maganar batayi duba ba" Na ce da ita, "Kinga a kwan a tashi girma kike" Kuma ke mace ce rayuwa gajera kike Idan nace ki jira yan gidanku su ya suke Gani suke in ma kin jira ni ba so ne ba Da kyal na shayo kan yar uwa gwana ta Farinciki na sadaukar wa rayuwar ta Yanzu ta yo auren ta tai zaman ta Na gode Allah banzo a masu san zuciya ba Bata yaudare ni ba Ban yaudare ta ba