Kalmar So
Hamisu Breaker
3:16Wama nake nema? Wama nake nema? Wama nake nema? Bani dama, na bayyanar da komai Kokarina, kan sanki kar a yada ni Gonar so, nai fure da mai-mai Nai bajinta kan sanki kar a kauda ni Kinga dake zana zauna Sai ki rike min amana Sanki yanan a raina Kaso a soka shine soyayya, zancen gaskiya Ashe son masoyi riba ne, zancen gaskiya Kisan mai bajinta shine yake tausasa zuciya Idan kika yarje masa gareki nasan ba sha wuya Batunsa amsa mishi Farin ciki kisa mishi Lalai haka shine burin duk masoyi na gaskiya Zuciyata na jikinki kin sani Gimbiyata, rayuwa dake zanyi So nakeyi, kiyi mini lamuni Sai mu zauna, so ya zama a tsakani Ni Hassan ke Usaina So ya samar da kauna Sai ki setan tinani Kwarai sanki ya dauka a zuciyarsa guda daya Farin cikinsa burinsa ke dashi ku zamo daya Hadinku zaiyi dai dai, ku zarce dukanin masoya Zaku kere duk sa'ani, ke dashi kun zamo tsintsiya Bi ma'ana madauri daya A rayuwarku gaba daya Ke yarda da duk batunsa, ki bishi Don ku zauna gu daya Uhmm-mm-mm-ah La-la-la-la Ahh-hh-hh-ah