Gobe Ma Ranace
Abubakar Sani
9:22Na gano tsauni ya nisa Zo ka dauke ni daura ni Mafaka ta ce Makaranta ce Nan kika dace Kar ku taka (ah wai) Kar da ku takan sirrika na Da nayi ajewa Kar ku taka (ah wai) Kar da ku takan sirrika na Da nayi ajewa Gane nufi na, karda ki ce a'ah farin ciki na Babban kalami, da ya fito baka shi zaki auna Tilas ne a saba, a rayuwa in anka zauna Ta so taho mu tafi, daren jiya dake na kwan a cikin mafarki Zaki na harshe, shi zaka ban na suda na tande Gonar fulawa, indai ka shuka zana hude Kyawu na fata ta ka zo ka shafa kan ta hude Kalma mai kyan harafi cikin lam a nan ka jefa baka masauki Ki riken flower, ki sa idon ki cikin ido na Ki sakan alawa, nima na tsotsa farin ciki na Soyayyah da zafi, ammah irin ta ki tafi kuna Kin zo da kyan lafazi, fada masu ki bayyana masu nine sadauki Ka sa zan narke, kamar digar kankara a fata Ka fito ma hantsi, kamar fitar rana daminta In ka fada min, cikin kwakwalwa ta ya zauna Shigar da zan maka ce amsar abinda duk ka fada sadauki Kar ku taka (ah wai) Kar da ku takan sirrika na Da nayi ajewa In na rike ce, zan mace, kece Zuciya ce, tace min na nace Ai kece mace, wacce ta dace Ni dai nace, kai ne ka dace don soyayya ce Idan kuma zan zauce, kece Ce-ce-ku-ce zan ce mara tushe, an ce Sai na nace, in dai an ce, dani kika dace Soyayya ce mai sa kyan jiki, haba! Kar ku taka (ah wai) Kar da ku takan sirrika na Da nayi ajewa Kar ku taka (ah wai) Kar da ku takan sirrika na Da nayi ajewa Kar ku taka (ah wai) Kar da ku takan sirrika na Da nayi ajewa