Duniya Labari
Hussaini Danko
3:55Zaurance a Hausar magana fira ce Da kwatance ake bai wa zukata wuri Zaurance a Hausar magana fira ce Da kwatance ake bai wa zukata wuri Salon mu da tafa-tafa so na bar miki yanmata Sanar mini in kin karba in ga na hada yarda ta Dake naga yayi dacewa inga na hada jinga ta Ki yarda ki lamunta Kizam mini mata ta Muyi rayuwa Mu ga shakuwa Idan na taho, kin taho, su taho gare ni fuskanta Suna dauke algaita Na busa ga mai tsafta Ke zaki zami mini yar shagwaba zaman ki gida na Na lura dake komai kika so nai miki na dau alkawari Zaurance a Hausar magana fira ce Da kwatance ake bai wa zukata wuri Tsaya kaji babban zance kar nasa ka a kokwanto Da zuciya ta lamunce dole za'a ga daidaito Sanar maka na tantance sirrika duka zan kwanto Na kai maka karshen zance kai ka zam mini sha zanto Na gamsu ni Ka rike ni ni Kai nake gani Da tuna-tuni Mai son ya raba zai ja rigima da bata da rana Jini na jiki ya kamu da so da gaske da kai zan alfahari Zaurance a Hausar magana fira ce Da kwatance ake bai wa zukata wuri Yau harshe fadi soyayya, kunne saurare Saurare, na jere, a zaure, gamu tare, turare (turare, turare) (Turare, turare) Ki tsaya, na biya miki darusa rike mini Tafiya, gajiya, ko daya bata zo mini Aniya, ki iya zaki ki kyautata mini Ni nayi sabo, da kai nayi yarda In kaga zanbo, zanen ta ka shaida In kaji zambo, nan ka mai yarda Duk yarda ka debo, kauna tayi tsada Dole cikin maza da kai zan hada hanzari Zaurance a Hausar magana fira ce Da kwatance ake bai wa zukata wuri Kinyi ina gani, zan baki kulawa Koda ga sansani, kin kayi fitowa Masu idon gani, ke zasu yabawa Amsa kiran wani, toh kar ki iyawa Inda kace na zo, nan zana tsayawa Tunda a zuciya, kai daya na ajewa Nayi maka gun zama, don bani cirewa Kar kayi tagumi, da gaske nayi ma wuri Zaurance a Hausar magana fira ce Da kwatance ake bai wa zukata wuri Zaurance a Hausar magana fira ce Da kwatance ake bai wa zukata wuri