Magulmaci
Mynmaster Productions
5:22Amma mai akwai da babu Duka dangantakanku dai-dai Allah ike fadan haka Bani nake fada ba Dani nake fadan haka Da sai ku karyata ni Kai mai akwai da babu Idan kai gida talatin Cikin guda zakaje ka kwana A daki guda ka kan kwan A gefen gado guda dai Haka nan wanda bai da komai Gida guda za ije kwana A daki guda yakan kwan A kayin kwarauni fale Toh in gari ya waye Tanan duka dangantakanku dai-dai Kai mai akwai ka gane In kana takaman akwai ne Baka sanya hula goma A kanka kai dai Sai kasa guda dai Haka wanda baida komai Shima issa guda dai Toh malam idan ka duba Tanan duka dangantakanku dai-dai Kai mai akwai ka gane In kana takaman akwai ne Baka sanya takalmi goma A kanka kai dai Ai da an gano ka Sai ace "ga mahaukaci nan" Sai dai kasa guda dai Haka nan wanda baida komai Shima issa guda dai Toh malam idan ka duba Tanan duka dangantakanku dai-dai Kai mai akwai kagane In baka dan misali Da nonon sule talatin Da nonon kobo talatin In an hada ka gane Sai kaga su duk furansu dai-dai Kai mai akwai kagane In baka dan misali Da agogon jaka talatin Da agogon sule talatin In wanan ibada loto dai-dai Wachan ibada loto dai-dai In za'a je gida toh Sai kaji duk sunan su agogo In baku dan misali Ran komuwa ga Allah Kai mai akwai kagane Rami guda akan tona Ka tina ba'a tona goma A fari za'a nan-nade ka Hakan nan wanda baida komai Ran komuwa ga Allah Yadi biyar fari dai A shi za'a nan-nade shi Rami guda akan tona Ka tuna ba'a tona goma Toh malam idan ka duba Tanan duka dangantakanku dai-dai Shi Allah huwal lazina Yayi larabawa Yayi indiyawa Yayai yo mutan amurka Allah huwal lazina Yayai haka domin mu gane juna In mudin shine In mai Kai mai akwai kagane In mudin kana dashi ne Ka shirya haibi Bayanka sunji dadi 'Ya'yanka sunji dadi Kowa izo issa mu Kaga ran komuwa ga Allah Wallahi tayi dadi In mudin kana dashi ne Baka taimako ga kowa Burinka kai ka bata Kaima kazo ka kare 'Ya'ya suzo su kare Mata suzo su kare Dukiya ma tazo ta kare Kaima kazo ka kare Kaga ran komuwa ga Allah Ranan dakai da babu Duka wallahi babu ban-ban