Babban Yarinya

Babban Yarinya

Umar M. Shareef

Альбом: Babbar Yarinya
Длительность: 4:06
Год: 2017
Скачать MP3

Текст песни

Babbar yarinya nayi sa'a
Na zamo auta cikin maza
Haduwar mu dakai shine sa'a
Bayani dace a yan mata

Hankali ke sa ayo girma
Natsuwa mataki cikin girma
A gurin ki dukkan su kin sama
Ko a cikin sunan ki kwai girma
Babbar yarinya lakabin ki, ke na raba don nayo girma

Duhu mai dusashe haske dukkan mai ido shi zaya fadan ma
Indan akwai ka ba'a batu na, ganin mu dakai ke karan girma
Manyan yara da sun ganka, su zo da sauri kai su karrama

So da kauna shi nake nema
Indai a guna ne tuni ka sama
Lallai gare ki ina da alfarma
Ko wani ka kawo ka sani zanyi ma
So yakai so tsakanin mu, bana gajiya gun yi miki hidima

Haduwar mu dakai shine sa'a
Bayani dace a yan mata

Haduwar mu dakai shine sa'a
Bayanin dace a yan mata

Nazari nayo a kanki, da tabbacin banyin nadama
Kinyi min shimfida ta fuska, zahiri ta zarce tabarma
Nayi rawa a gaban ki na taka, zo kimin naki sallon kema
Allah nunan masoyan mu, ka tsare mu sharri na yan gulma

Kayo nisa cikin raina, ba'a hangen ka bare a cimma
Ganganci ne a ce za a iske ka, ko dan gajiyar tafiya a suma
Tunda na tsinke zaren burki, yan samari sai kuyi ta himma

Babbar yarinya nayi sa'a
Na zamo auta cikin maza
Haduwar mu dakai shine sa'a