Hisabi

Hisabi

Umar M. Shareef

Альбом: Masoya
Длительность: 3:41
Год: 2017
Скачать MP3

Текст песни

Hisabi shi nayi wa kaina akan so
Makoma ta zamo da dadi, iyeh-iyeh
Hisabi shi nayi wa kaina akan so
Makoma ta zamo da dadi, iyeh-iyeh

A kallo ke nake wa kallo in kara
Kalami in kikayi batu dole a saurara
Wajen kwalliya ko dukka mata sun sara
Mukami babu wata sai ke

Mafarki wataran yakan zama hakika
Ka girba sai abinda kaine ka suka
Alkhairi shi nake ta fata na saka
Domin baya na ya zam da haske

Akwai watarana ina jiran ta tazo
Da zanga iyaye abokanai dandazo
Ana raba goron daurin aure anka zo
Sai walimar shinkafa da wake

Hisabi shi nayi wa kaina akan so
Makoma ta zamo da dadi, iyeh-iyeh

Hisabi shi nayi wa kaina akan so
Makoma ta zamo da dadi (iyeh-iyeh)

Mai nema karya fidda ran zaya samu
Kamar ni na sani akwai lokacin mu
Idan Rabbi yayi nufin sa tilas a barmu
Da igiyar mahassada mu tsinke

Ba canjin ra'ayi, a so kine dai nayi wa alkawari
Duk zafın yanayi, bani gudu indai kina a gari
Ba nayin kwadayi, wulakanci na guje fita hadari
Halili gun nema na kuke

Kamanni mukayo da kai na duba haka
Da halin mu iri daya ba farraka
Ashe dole zaman mu zaiyi dadi haka
Mu more muci duniya da tsinke

Hisabi shi nayi wa kaina akan so
Makoma ta zamo da dadi, iyeh-iyeh
Hisabi shi nayi wa kaina akan so
Makoma ta zamo da dadi, iyeh-iyeh