Barauniya
Umar M. Shareef
3:34Idan kika ce nine Ba zan baki kunya ba Nima zana ce kece zabi na Tunda har kace nice Ba zan baka kunya ba Nima zana ce kaine zabi na Kece wacce nake yin nuni, sinadari na Tarayya dake zan tare, mahadi na Ungo na sako miki tsani, shigo gida na Babu mai mini kallon raini, uwargida na Nasan in na aure ki Bazan kwana da yunwa ba Tun da kin kware gun girki Iyali na Soyayya muke don Allah iya sani na Shiyasa muke dada danko tare da juna Alkhairi muke so mu kulla da masoyi na Koda yaushe in nayi sallah a addu'a na Allah sa nazam taka Mai kula da hakkin ka Farin ciki zan tara maka A daki na Munyi gaba mun wuce Munyi nisa mun bace Kamar hannun agogo Bani jin bugun ice Na yarda in mace Na kai ga bango A mike babu karkace Ba rabewa kai kace Waka nake da dango Zanyi yadda kai kace Ni masoyiyar kace Jarumi daban da rago Soyayyar ki ba rai ni Bazan yi asara ba Gun biyan kudin dinki Iyali na Idan kika ce nine Ba zan baki kunya ba Nima zana ce kece zabi na Tun da har kace nice Ba zan baka kunya ba Nima zana ce kaine zabi na