Lelewa Tini Tini
Adam A. Zango
4:18Sabon kidan kaduna Muji tamburan kaduna Sabon kidan kaduna Muji tamburan kaduna Sabon kidan kaduna Muji tamburan kaduna Sabon kidan kaduna Muji tamburan kaduna Kaduna Adam na shigo gari Yaro ne adon gari Ya shigo garin Kd A garin kano akwai naira Sannan muna da sarki na zazzagawa (eh) Adam zango mai gari Yaro ne adon gari Ya shigo garin Kd A garin kano akwai naira Sannan muna da sarki na zazzagawa Oyoyo (Iyye) A Zango oyoyo (maza-maza) Oyoyo (iyye) A Zango oyoyo (gani nan) Oyoyo (na'am) A Zango oyoyo Salam-salam-sallama Sallama gareku masoya Gareku nayi jinjina godiya nike da biyyaya Adon gari nafito zango ban kama da kiyayya Duk halin da nashiga kuzo ku rungume ni masoya 'Yan kaduna mun hadu mata da maza muyi niyya Muje mu neman karatu shine tushe na biyayya Ilimin mu na boko mu rike har islamiyya Kai babba da yaro Tsoho har da tsohuwa Mai kudi da talaka Mai gida da mota Mai gida da AC Ilimi shi zamu bukata Idan naga dama-in naga dama Idan naga dama (ina zaka kwana) In naga dama a garin jaji zan kwana (toh je ka kwana) Idan naga dama a rugasa ni zan kwana (sun baka dama) Idan naga dama a unguwar rimi zan kwana (kasamu dama) Kuma in naga dama a mando ni zani kwana Adam zango mai gari Yaro ne adon gari Ya shigo garin Kd A garin kano akwai naira Sannan muna da sarki na zazzagawa Oyoyo (Iyye) A Zango oyoyo (maza-maza) Oyoyo (iyye) A Zango oyoyo (gani nan) Oyoyo (na'am) A Zango oyoyo Kaji bugun tambari gaisuwa ga sarkin zazzau (Ameen) Zaki ka sha gaban kura sarki mai zazzau (Ameen) Ka sha zamanka ka huta duk wani sarki ya biyoka (Ameen) In kadau kwalliya kowane sarki kallonka (Ameen) Kaine jiya kaine yau gobe muna bayanka (Ameen) Sarkin zazzau adalin sarki na gaisheka (Ameen) Duk jama'ar zazzau da kaduna muna son barka) Kai hani da cuta (Ameen) Kai hani da zamba (Ameen) Kai hani da cha-cha (Ameen) Kai hani da sata (Ameen) Toh mukama sana'a sarkin zazzau zai murna Idan naga dama-in naga dama Idan naga dama (ina zaka kwana) In naga dama unguwa na kanawa zan kwana (toh je ka kwana) Idan naga dama unguwa na sanusi zan kwana (sun baka dama) Idan naga dama askwalaye ni zan kwana (kasamu dama) Kuma in naga dama cikin kabala ni zani kwana Adam zango mai gari Yaro ne adon gari Ya shigo garin Kd A garin kano akwai naira Sannan muna da sarki na zazzagawa Oyoyo (Iyye) A Zango oyoyo (maza-maza) Oyoyo (iyye) A Zango oyoyo (gani nan) Oyoyo (na'am) A Zango oyoyo Karo da karo sai rago dan akuya baza ya iya ba Sarki kake babban bango kowa ya barka yafada kango Ga baya goya marayu wallahi kazama babban jigo Ga agogo sarkin aiki Namadi Sambo babu kamarka Kudi da kudi sai Kd wurin zubar da jini sai kwata Kida da kida sai studio in kaga rawa sai zango Ina 'yan makarfi 'yan kauru 'yan sobe da giwa ku jini Ina 'yan sanga the people din jama'a 'yan kaciya ku bini Ina 'yan gayun ABU Ina babies ABU Ina 'yan state university Ina 'yan poly sai kuzo ku ganni Eh ohohoho Idan naga dama-in naga dama Idan naga dama (ina zaka kwana) In naga dama sabon tasha zan kwana (toh je ka kwana) Idan naga dama rafin guza ni zan kwana (sun baka dama) Idan naga dama barnawa ni zan kwana (kasamu dama) Idan naga dama rigachikun ni zani kwana Adam zango mai gari Yaro ne adon gari Ya shigo garin Kd A garin kano akwai naira Sannan muna da sarki na zazzagawa Oyoyo (Iyye) A Zango oyoyo (maza-maza) Oyoyo (iyye) A Zango oyoyo (gani nan) Oyoyo (na'am) A Zango oyoyo (muje-muje-muje) Sabon kidan kaduna Muji tamburan kaduna Sabon kidan kaduna Muji tamburan kaduna Sabon kidan kaduna Muji tamburan kaduna Sabon kidan kaduna Muji tamburan kaduna Kaduna Adam na shigo gari Yaro ne adon gari Ya shigo garin Kd A garin kano akwai naira Sannan muna da sarki na zazzagawa (eh) Na shigo gari Lallai kuna da girma Eh nine-nine