Soyayya
Hamisu Breaker
Hayyaa-aa-aa maza Hayya kai Baitin girma anyi wa dan girma Munkaila Gwaska yau zan gaisarwa Ya ka dakata ni Kidan sako mini In gaida maza In gaida maza Eh, Hamisu Breaker zan maka waka Ta alfarma Gwaska ka zama gwanin al'umma Yau na jinjigo tsayuwar waka da zance zanyi shi gun mai hanun dama Gwaska ina kiran ka da kima Da girma, sunanka yafi min dala girma Tillas in jinjina wa gwarzo Mai binka ya wuce yaci kanzo Gwaska mutun gari ke yabon ka Naji sanan nace dasu zan fara nima Ka kai a jinjina maka domin Halayenka sunyi baka yin banbarma Gwarzo maza suna bayan ka Wane zaya ja dakai ya fada koma Wasu baituka nayo tsaro ma Ka tarban da shimfidar taburma Dan Hausa bayi kyamar Hausa A Kanon dabo na kwana zana karya da fura Yayan mu wallah ka kaisaita Ka wuce duk makiyanka yanzu basu da saura Wasu kanka har sun zauce Suna bori harda yin farar dafara Kwantar da hankali yaya na Ba dai mutum ba wallah sai rabbani Wa zaya ja da ikon Allah Idan ka fito duk mazan sa buya Gwaska kainuwa tashe daga Allah Waye zaya cire ka ni nace yayi karya Shugaban matasa kai ne Gwaska Fagen taimako naga yaya baka sanya Wa zaya kushe bayan kwarya? Gwaska kazama gatan maraya Gwaska kaine katar kama kada Batai hanu ya kasa ba kai masa kwari Kaine ka maida Naira yayi Wajen kyauta naga kai kanayi da sauri Kyautan har akan makiyanka Ka nai musu riga kaci dasu tun a fari Fuskarka na cike da anuri Gwaska ni naga ka wuce wa su kwari Halin kwarai kawai zan furta Akan Gwaska banyi kirkira ko dai ba Mai hakuri kanada kamala Da girmama manya akan hakan kayi shura Gwaska kasan mutuncin jamma'a Mai alkawari kai kadai ka wuce tantabara Danbi kake ka wuce saura Baitinka yanzu, yanzu na fara Sunayenka yanzu su zan jera In sanar da mutan gari su shaida suma Munkaila jinjina gareka Dan albarka babu mai shigar mu a tsara 'Dan manya jika gun manya Gwaska haka ne bazana boye ma ba Ku ban amsa kuwa dan zanyi kira Ishaq mutumina zan kira kuyo saurara Mai gida Ishaq kai ka shahara Dole in yo maka jinjina salon ban girma Gwaska yace yana ji dakai ne Nima naji da kai yar baituka nayi ma Nasan ina kira sunan ka Kudi zan deba da kyautukan alfarma Sannu hidimar al'umma Ishaq kana da halin girma Gaisuwa zanyi gun matan ka Hakan zanayi naga yafiye min nima Uwar gida dole na gaishe ki Domin na gaishe ki na yaba ya kema Nai baituka a sunan 'dan ki Ga wata sabuwa yanzu nai bugawa itama Amarya tillas in gaishe ki Halayen abin yabo garan ne nima Domin kai a yaba ma da dadi To gidan ku an saba yi mini alfarma 'Ya'yanku yanzu su zan gaida Domin suma bazana je basu ba Salma ina yabo mai girma Mubarak ina yabo gun kaima Tahir ina yaba ma kaima Yan uwansa yanzu su zan gaisar Bi ma'anata yan uwa gun Munkaila Gwaska Alhaji Tahir na gaishe ka Tillas in yaba dan kana yi mini alfarma Hajiya Maimuna na gaishe ki Ga jinjinar yabo gareki kema Balki Bare star na gaishe ki Kema nai jinjina da hanun dama Sani dakta kaima gaishe ka Ga jinjinar yabo ga mai alfarma Ishaq bazana je ba kai ba Domin yabo kana min nema Tamburana sun chaja domin mama Tillas in kas murya in ambaci mama Maman mu jinjina bazan fasa ba Dan dan kwarai nake ba dan sauna ba Baza'a mini kara yazamo ban furta ba Mama a wakar suna nazo da bara ta Nace kiyi min alfarma nazam 'da gunki Kika ce kin mini nazama dan gida a gurinki Naji dadi shine gani ba nasaba ba Karshen zancen dai 'da da uwa baza'a raba ba Karshen magana ta naga ko furta ba Sunan mama hajiya yaya Amina ce Idan kasan ta akwai su kama mama mai fara'a ce Yabon mama agareni hakan kamar damara ce Sunana Hamisu S Breaker wake Karshen magana ta mama addu'a a takaice