Yaushe Zaki Dawo
Umar M. Shareef
3:41Ana dara ga dare yayi Da nasara a guri na ni Ana dara ga dare yayi Da nasara a guri na ni Farin ciki na A kan ido na Cike dani nine gwanin ki Ki bani kauna In zo mu zauna Farin ciki shi zana baki Muje in gaida yan'uwan ki Su san da nine zasu bai wa mata Ko ban fadi ba Ba a musa ba Kasan cewa kai nayi zabi Ni kai na zaba Na cewa baba Tun-tuntuni ni kai ne madubi Nayi addu'a Allahu Rabbi Idan ya amsa mu zam miji da mata Tafiyar da akeyi a sannu Za ayo nisa chan a lula Hankali ya zarce idanu Ilimi shi na kira fitilla Ina ta shela Kuzo ku kalla Farar diya ta sace zuciyata Ana dara ga dare yayi Da nasara a guri na ni Ana dara ga dare yayi Da nasara a guri na ni Uwar jiki an san lafiya ce Kai ka dau matsayin ta gare ni In babu kai ni mara lafiya ce Magani kai ne zaka bani In ka kula ni Kowa ya bar ni Nasan da cewa zaka bani gata Na baki duka daukacin lokaci na Gun ka dukka na karkato hankali na Ke nake wa gini ki zauna gida na Zana bika a sannu ya malami na A so da kauna Iya sani na Kamar babu cikin maza da mata Ana dara ga dare yayi Da nasara a guri na ni