Notice: file_put_contents(): Write of 649 bytes failed with errno=28 No space left on device in /www/wwwroot/muzbon.net/system/url_helper.php on line 265
Hamisu Breaker - Gwaska | Скачать MP3 бесплатно
Gwaska

Gwaska

Hamisu Breaker

Длительность: 7:04
Год: 2018
Скачать MP3

Текст песни

Hayyaa-aa-aa maza
Hayya kai

Baitin girma anyi wa dan girma
Munkaila Gwaska yau zan gaisarwa
Ya ka dakata ni
Kidan sako mini
In gaida maza
In gaida maza

Eh, Hamisu Breaker zan maka waka
Ta alfarma Gwaska ka zama gwanin al'umma
Yau na jinjigo tsayuwar waka da zance zanyi shi gun mai hanun dama

Gwaska ina kiran ka da kima
Da girma, sunanka yafi min dala girma
Tillas in jinjina wa gwarzo
Mai binka ya wuce yaci kanzo

Gwaska mutun gari ke yabon ka
Naji sanan nace dasu zan fara nima
Ka kai a jinjina maka domin
Halayenka sunyi baka yin banbarma
Gwarzo maza suna bayan ka
Wane zaya ja dakai ya fada koma

Wasu baituka nayo tsaro ma
Ka tarban da shimfidar taburma
Dan Hausa bayi kyamar Hausa
A Kanon dabo na kwana zana karya da fura

Yayan mu wallah ka kaisaita
Ka wuce duk makiyanka yanzu basu da saura
Wasu kanka har sun zauce
Suna bori harda yin farar dafara
Kwantar da hankali yaya na
Ba dai mutum ba wallah sai rabbani

Wa zaya ja da ikon Allah
Idan ka fito duk mazan sa buya
Gwaska kainuwa tashe daga Allah
Waye zaya cire ka ni nace yayi karya
Shugaban matasa kai ne Gwaska
Fagen taimako naga yaya baka sanya

Wa zaya kushe bayan kwarya?
Gwaska kazama gatan maraya
Gwaska kaine katar kama kada
Batai hanu ya kasa ba kai masa kwari

Kaine ka maida Naira yayi
Wajen kyauta naga kai kanayi da sauri
Kyautan har akan makiyanka
Ka nai musu riga kaci dasu tun a fari
Fuskarka na cike da anuri
Gwaska ni naga ka wuce wa su kwari

Halin kwarai kawai zan furta
Akan Gwaska banyi kirkira ko dai ba
Mai hakuri kanada kamala
Da girmama manya akan hakan kayi shura

Gwaska kasan mutuncin jamma'a
Mai alkawari kai kadai ka wuce tantabara
Danbi kake ka wuce saura
Baitinka yanzu, yanzu na fara
Sunayenka yanzu su zan jera
In sanar da mutan gari su shaida suma

Munkaila jinjina gareka
Dan albarka babu mai shigar mu a tsara
'Dan manya jika gun manya
Gwaska haka ne bazana boye ma ba

Ku ban amsa kuwa dan zanyi kira
Ishaq mutumina zan kira kuyo saurara
Mai gida Ishaq kai ka shahara
Dole in yo maka jinjina salon ban girma

Gwaska yace yana ji dakai ne
Nima naji da kai yar baituka nayi ma
Nasan ina kira sunan ka
Kudi zan deba da kyautukan alfarma
Sannu hidimar al'umma
Ishaq kana da halin girma

Gaisuwa zanyi gun matan ka
Hakan zanayi naga yafiye min nima
Uwar gida dole na gaishe ki
Domin na gaishe ki na yaba ya kema

Nai baituka a sunan 'dan ki
Ga wata sabuwa yanzu nai bugawa itama
Amarya tillas in gaishe ki
Halayen abin yabo garan ne nima

Domin kai a yaba ma da dadi
To gidan ku an saba yi mini alfarma
'Ya'yanku yanzu su zan gaida
Domin suma bazana je basu ba

Salma ina yabo mai girma
Mubarak ina yabo gun kaima
Tahir ina yaba ma kaima

Yan uwansa yanzu su zan gaisar
Bi ma'anata yan uwa gun Munkaila Gwaska
Alhaji Tahir na gaishe ka
Tillas in yaba dan kana yi mini alfarma

Hajiya Maimuna na gaishe ki
Ga jinjinar yabo gareki kema
Balki Bare star na gaishe ki
Kema nai jinjina da hanun dama
Sani dakta kaima gaishe ka
Ga jinjinar yabo ga mai alfarma

Ishaq bazana je ba kai ba
Domin yabo kana min nema
Tamburana sun chaja domin mama
Tillas in kas murya in ambaci mama
Maman mu jinjina bazan fasa ba
Dan dan kwarai nake ba dan sauna ba
Baza'a mini kara yazamo ban furta ba
Mama a wakar suna nazo da bara ta
Nace kiyi min alfarma nazam 'da gunki
Kika ce kin mini nazama dan gida a gurinki

Naji dadi shine gani ba nasaba ba
Karshen zancen dai 'da da uwa baza'a raba ba
Karshen magana ta naga ko furta ba
Sunan mama hajiya yaya Amina ce
Idan kasan ta akwai su kama mama mai fara'a ce
Yabon mama agareni hakan kamar damara ce

Sunana Hamisu S Breaker wake
Karshen magana ta mama addu'a a takaice