Kanwata
Hamisu Breaker
3:09Eh idan gaji gugiya kasani akwai labari Bayyanin gaskiya wanda ba'ayi yin kari Labarin mai sona ta gaske zanyi a tsari Duk wanda yasan ni da ita yasani don mun saba Akwai so a cikin zuci wanda bashi da riba Kaso wanda yake son wani bakai dace ba Amma ni soyayyar danayi banyi kure ba In naso wanda taso ni san da banyi zato ba Kafin na kaiku da nisa Dorayi karama nake Unguwar Bello a nan nake sana'ar dinke A inda nake kuma gidansu ma a layin yake Gani na farko ta danayi zuciya ta harba Shekaru masaikaita kaunar mu tayo girma Yi mukeyi tare gidansu an sallama Tazo da safe da yamma dare gidansu na koma Tana burge kowa masoya duka sun yaba A kwan a tashi muna kara shakuwa mai tsanani Tana yin wanka tayi kwalliya du dan ni In ko tayo kunshi tai flower duk dan nine Idan tazo nunan bani nan bazata tsaya ba Masoyiyata na tara yan kudinta tabani Tana yi mini hidima abinda zanyi tai mini Toh matsalar farko ba kudi na aure gare ni Gashi ta girma a lokacin da ban aune ba Gidansu an ce, "Na fito idan da gaskiya nake" Kuma ni santa a zuci na riga na rike Idan aka fadan inbar ta kuma kuka nake Raina ya bacci ayi fada dani koda ba'a so ba Lalai akwai al'ajabi a so na gaskiya Da kaina nai mata maganar dazata waiwaya Nace tayo aure zaifi mata gaskiya Tace dani nabari maganar batai duba ba Nace da ita kinga a kwan a tashi girma kike Kuma ke mace ce rayuwa gajera kike Idan nace ki jira yan gidanku su ya suke? Gani in ma kin jirani ba so bane ba Da kyar na shawo kan yar uwa gwanata Farin ciki na sadaukar wa rayuwarta Yanzu tayo aurenta tai zaman ta Nagode Allah ban zo a masu san zuciya ba Bata yaudare ni ba Ban yaudare ta ba