Ana Dara
Umar M. Shareef
3:30Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya Ciki na samo ki nayi nasara a so ba damuwa Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya Ciki na samo ka nayi nasara a so ba damuwa Ba zan so ba, koda wasa bazan barki ba Na duba, a ciki ni banga kamar ki ba Mun saba, ni da ke ba za'a raba mu ba Mun caba, in akayi aure munyo gaba Shine daidai tun daga nan mu bar yin fargaba Ke na so tunda ni kika so hakan ne kyautuwa Kai ne farko, kai na cira cikin su mazan gari Mai karko, wanda bai sanya ni inyo jiri Muyi baiko, ni da kai tun tuntuni nayi shiri Da ka aiko, iyaye sai ayyiri-yiri A cikin auren nayi shiri na daukan hakuri Na yarda da kai zan zauna iyakar rayuwa Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya Ciki na samo ki nayi nasara a so ba damuwa Lallai, kauna ce da so, kin nuna gare ni Ko anki ni so, kece mai kula ni Nayi dace a so, abokai na kuji ni Ke nafi so a so, in an tambaye ni Bana kallon kowacce 'ya cikin yanayi na so In ba ke ba banda abokiyar yin rayuwa So na dandana, zaki ya rufe ni In na rissina, masoyi na daga ni Ni zan adana, sirri in ka bani Naki in bayyana, ko an takura ni Sam ba kowa idanu ba wanda suke gani Kai ne dai wanda tun asali muka yo shakuwa Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya Ciki na samo ki nayi nasara a so ba damuwa Fadli falala anyi wa dan Adam sai godiya Ciki na samo ka nayi nasara a so ba damuwa