Sakon Amarya
Hamisu Breaker
3:58Ehhhhhh Ehhhhhh Ahhhhhhh Tin tana yar karamar ta nake yin tsokanarta Nake cewa mamanta 'yar nan za'a bani ita Idan ta fito kumah ni ne nake fara kula ta Da wasa nake nikuma a zuciyata Ehhh idan na ganta kumah ni nake yabonta Ina rakata har cikin makaranta Na faranta dukanin rayuwarta Na dauke ta yar uwa kumah kanwata Har ta girma a shekarun ta a takaice Harkokina sun kara yin yawance Lukutana kumah sunyi min karance Na chanja tsarin rayuwa ban sani bah Duk abokai munyi rata dasu nei Haduwar mu dasu kumah tai wuya nei Wasu basu da lambar dazasu kirani Tina dasu haka ban iyo bah Wayyo ashe cikin matsala ne ni na barta Kullum tinanina kawai ne a ranta Ta sanya soyayyata a zuciyarta A zatonta da gaske nima na so ta Kullum akaina tanayin wahalta Gashi ta rasa layin kiran wayata Kumah ganina yazam abun wahalta Ni koh tin har na manta da ita Kwanci tashi tana kara shan wuya Shekaru da yawwa tana bibiya A gida an rasa gane gimbiya Gashi yau akaina ta samu cuta Wata rana, ranar talata Banje aikina ba don zana huta Na fito waje sai ga yar aiken ta Wai ana nema na tazo da kanta Sai tace mini sako ne aka bata Wai naje gun, babbar kawarta Wai tana asibiti zanaje na ganta Yanzu yanzu tace min ana bukata Ehhhhhh, nan da nan ni kumah sai natafi gurin ta Ina shiga sai kowa na gun ya barta Nan aka barmu a dakin dani da ita Na tambaye ta shin yaya jikinta Sai tace mini wai inji tausayinta Akan sona nei take yin wahalta Gashi ta kamu da ciwo a zuciyarta Kumah ni kadai ne magani ta Inko kaki toh ni zan hakurta Zuciyarka sam karka takurata Zan mace kawai ina jin na huta Kasa a ranka kaine sanadiyata Hankalina a take sai yayai dimauta Duk tinanina take ya gurgunta Tausayinta yazo mini zuciyata Take santa ya mamaye zuciyata Matsalar gashi nakai kudi ga wata Ranar auren mu tini an saka ta Ga bikin namu kumah ya kusanta Ga bayyanin da ita kumah ta furta