Gudun Wuce Sa'A
Nura M Inuwa
5:40Zuciya zana baki kyauta ki adana So na taho hadin zumunta dani da ke Zuciya zana baka kyauta ka adana So na taho hadin zumunta dani da kai Nayi mafarki nayi gamo, nasara ta ta biya Amsa kalaman zuciya Na baiwa sa'a sunan rabo, kika yi min na tsaya Kinga a rai kin tausaya So da aminta zan fada, kika amsa kin iya Zuciya tabar shan wuya Na zama dan almajiri, da barar so na biyo Ke na kira da zinariya, da kalaman gaskiya Kayi sa'a babbar rabo da kira na na jiyo Sai ka matso zan bayyana Zuciya ta amsa yabon da kake sai na biya In da kaje zan dangana Naji kalamai ka fada, da nake son kwaikwayo Zana rike in adana San da kazam min mallaki, nabi in dan sunkoyo Duk ladabi na zana ma furucin so ka biya Na maida hankali na kan ki Rai na da zuciya na baki Da zaki so matso in gan ki Kin min kaso kiban hannun ki Ranar mu ce a zo kallon ki Ribar mu ce da na aure ki Mai zan yi don ya amfane ki Ni dai rike ni tamkar baby Ban zuciyar ka kayi min gurbi Sassan jikin ka in zam kuibi Kalmar yabon ka ce min hubbi Fuskar ka zuciya ke dubi Ruhi da kan shi kai yayi zabi Sai na gano ka zanyo shauki Ni na yarda na baki kaina Zuci kin ka nashe da kauna Wa yazo ya kushe ki zauna Ke kadai na saka a raina Zuciya ta dake zata kwana Ajiye kalaman yabo na, kariyar ki