As E Dey Do Me
Sani Danja
Mallakin ki zan zamo bayan aure Mallakin ka zan zamo bayan aure Jarabawar son ki anyi min naci Da soyayyar ki kullum nake barci Da soyayyar ki nake cin abinci Soyayyar ki ta cire kunci Ka sani a zuciyar ka na zauna ciki Ko mutuwa zata zo ta dauke ni ina ciki Duk inda na gan ka ni bazan boye ba In ka bar duniya bazan zauna ba Nina fidda wacce nake so a zuciya Idan zan fada maku sunan ta Mariya Soyayyah ciki nayi dace a gaskiya Na samu zabin Allah bani shan wuya Masoyin ki nine fari In same ki na cika buri Kice nine bani inkari Zuwa gun ki nayi da alkhairi Na kawo kalaman soyayya ki jiya Domin kiji dadi kiyi murna Mariya Farin ciki kaine mai baiwa Mariya Bakin ciki in nayi ka sakani dariya Dana gane ka sai inji na zama sarauniya Aure na dakai nasan bani shan wuya A duba cikin kauyen nan gaba daya Ba wacce ta dace masoyi ya Mariya Hafeez gani nazo, bani in baki Zabi kai na zabo cikin rayuwa Nayi duba zuciya ta, babu kamar ki Ke kadai ce kaf a mata, bata biyun ki A guri na kinyi gata, ba'a taba ki Ko'a bacci zani kwanta, sai da hoton ki Kece damuwa ta, da so samu A daura mana aure muyo rayuwa Dukan lokacina, kaina baiwa Rike min mana, ba adawa Dakai zani zauna, koda yunwa Zan sanya ka murna, babu rowa Kaine garkuwa ta, ba mai damu Yar lele ni na zamto cikin rayuwa Hauwa-Hauwa Kulu yanmata adon gari Hauwa, duk girman taro zana burge kowa Ke nake wa soyayya ta Ke naso ki zamto mata ta Zana baki dukkanin gata Guna baya ke a cikin yanmata Mai rabo allurar cikin ruwa Nine na zamo gwani na zarce wa tsara Ni kai na ciro fili na gada Mai kyan tafiya baya sanda Tsafta bai sa kaya da dauda Bana gajiya kai zana koda Burin Hauwa Kulu shine kayi farin ciki Zan zauna daman ka in dinga maka hira Fati, Fatima autar mata A raina babu yake har kullum Kai na zaba samari kuyo hakuri Na sanya ka cikin rai na baka guri Da ka nemi ka ganni zani zo da wuri Cikin rayuwa ta ka wuce gishiri Ni Fati zan yi wa mata kuri Don masoyi na ya wuce kanwan lasa Ni Zainabu Abu nake so, cikar burina Bayan ke bani da kowa cikin kalbi na Kyauta wacce zana fi so, ace mini gaka Tafiya garin dani nafi so, aure dakin ka Zance in za'ayi mini in so, a min maganar ka Bacin rai abinda bana so, inji an kushe ka A guna ka wuce kowa, kai baka da tamka In zam maka mata kaiko miji babban burina Ba rabuwa alkawarin ki na rike Gamon jini so haduwar mu yayo dai-dai Son ka ya shige a cikin rai ya kwanta Shi ya zam silar samun lafiya ta Da ke na so in kare a rayuwata In zam mijin ki ke kuma ki zama mata Zaman mu dole zai inganta Tunda ba muyi wa juna mugunta Kin zamo jini ni hanta Rabuwar mu zaiyi wuya na furta Farin ciki na sai karuwa yake Ku duba fuska yanayi na haka zaku gani ma A tsakanin mu babbar kalma ce gata Gwanin dadi a gurin furtawa soyayya Indai kasan gaskiya kar kayi karya Ranar wanka cibiya bata buya Indai na samo miya ban cin gaya Soyayyah nan zan tsaya banyi baya Kai zanyi jira duk daren dadewa Batun aure in ba kaine ba ya zama labari Kyawun ki shi ya saka ni na soki abar kauna ta Kyan ki shi ya saka ni naso ki zamo mata ta Kyawun ki wanda ya same ki shi ya zamo dan ganta Kyawun ki wanda ya same ki yayi wa mazaje rata Bawai kyawun da yake fuska ba Bawai kyawun da yake fata ba Bawai kyawun ki na kyan sura ba Wannan kyawun nan da bai gogewa, halayya