Da Auren Ki
Sani Ahmad
So na ne fah On the beat Soyayyar ki ce take mani yawo nidai Kabani labari Rayuwa tana son sirri sai dai Ka furta alkhairi Komai nawa sai kina nan zayai dai-dai Kana da kyan tsari Da zanai fushi da mai suka amman dai Ka jure yin tari Dukkan wani babban ba ya rike girma Kace da shi yaro yake In har rai da lafiya bama gaza nema A zuci tasirin yake Kin kana ganin ka toh kai mai jarkoma Ruwan iya gwiwa yake Shin an tashi lafiya sanadin hadin gulma Batun da in yanke yake Toh juya ki rausaya sai kin mini tsalle Gaban ka zan taka In ba ni ba kowa taho ki masa kwalele Ka daina yin shaka Zan goge gumin jiki na zan dada kyale Ka ja ni zan bika Kauna ke tsuma bana san sada tale Kawai muje harka Toh ya kinka tashi bacci dazu da safe? Ina tunannin ka Daure sa kai batun batun kar ki mini yarffe Ya zana ma haka? Kauna bata goguwa koda an tsufe Batun ka ba shakka Sirrin zuci yanzu zam bude shi a faife Ka kyale mai suka So a so ka magani Jani a son na kwantar hankali Da akwai rabo mai kallo zai taka dandali Kauna ta shige cikin zuciya Ta zauna da kyalkyali Wacca nakewa so tanai min so mai kyawu da tozali Ka san yau da gobe sai Allah dan shi ne da zamani Na yarje a bangaren soyayya nidai ka tai dani Bana tantama ina sonka kawai ni dai kula dani Kar watarana ni da kai mun saba kai mini lahani Na gane matsalar Ni ma matsla ta ce Na gane maganar Ai nima magana ta ce Rike ni muje inuwar Kai din ai kadara ta ce In har nayi kira sa kune saurari kalamai na Jirgin za ya cira Allah na iya maida dare rana Kyautar so ki rike zo karbi flower a hannu na Bini da kauna Ni kuma sai ki gwada mini soyayya So da amana na dau alkawari Ya zan sauya? Kar kaji zance Soyayyar ka ce take yi mini yawo In naga ba ke a kusa dani abun nai mini ciwo Kai ni misalin soyayyar ka a rai na na dauka Na biya allo dukkan wani karatu na dauka Mixed kobincus