Kyautar So
Umar M. Shareef
3:40Kauna ba zato ba tsammani ta shige cikin rai na Kai nake wa tayin so amshi kace kana so na Babu zata ba tsammani furucin ki kamar cikin barci Ni da ke ba zancen so sharadin ki bai kau ba Asalin soyayya kai na saka cikin zuci In na fara tunani naka sai na kasa yin barci In ka ambaci ya mace sai in ji ina cikin kun ci Zo ka bani ruwa na zuma kar ka bani mai daci Kai nayi wa tanadin soyayya Kar ka barni inyo jinya Riga ta son ka ne na sanya Dubi jiki na tai mini dai-dai Kece kika ce mini kalmar so kar na furta yanmata In ko na kuskura nayo hakan zaki tsane ni mun bata Niko da bani son haka nayi na'am na kira ki "kanwata" Nayi nisa a son wata ni a gani na zamu daidai ta Son ta nayo bata Hankali na ya karkata In bata zan hauka ta Dani da ita hadin mu yayi daidai Yau na bayyana ban boye ba cibi ina wanka Zancen dake cikina na fiddo shi fili ya sha iska Ka mamaye ni ka shiga rai na babu shiri ina bin ka Kar da kace dani baka so na zai saka ni nayi kuka Amshi makulli na ka tuka Ko'ina kace dani "Ta ka" Kowa ya kira ni "Matar ka" Zan amsa sunan haka ni dai Wacce nake so da soyayya Na sani tana akan hanya Zana nuna miki da gayya Aure na da ita na shirya Dube ta nan haka kiyi duba Madubi duba Da ita dani na saba Ba zamu rabe ba Hanta da jini a soyayya ba za'a rabe ba Fuskar dake ciki ce zabi na rike ni muje ke dai Na rude jin dadi Ka bani kauna Nagode, nagode Ka ceci rai na Kawo hannun ki nasa zobe na alkawari na Tun haduwar mu a farkon so tarkon ki ya kama kauna Nayi haka, nayi haka na nuna Bazan boye ba Nima nayi haka, nayi haka na nuna ka Ba jin kunya ba