Kusantu Dani

Kusantu Dani

Umar M. Shareef

Длительность: 3:27
Год: 2018
Скачать MP3

Текст песни

Zo kusantu dani
Zana rayu dake
Amana ta kaina zana baki

Zo kusantu dani
Zana rayu da kai
Amana ta kaina zana baka

Na aminta dake, mu zauna rayuwa tare
In za kiyo zance, ni kuma zanyi saurare
In baki tukwuici, zaba da kanki balango ko tsire?
Ki diba ki more, kauna ce tasa komai zanyi miki

Zo kusantu dani, zana rayu da kai
Amana ta kaina zana baka

Idanuwa ke suka buri, a koda yaushe su gani
Fuskar ki na dauke da nuri, kalle ni in zamma gwani
Cutar so dake yin ruri, ke kika zamto magani
Yanzu kowa ya ganni, banda damuwa sai tsantsar farin ciki

Abin kamar wasa, a son ka gani nayo nisa
Kuzo muyo gasa, yanmata sai kun sha kasa
Ni nuna zabin sa, haka nima shi kadai ne ya isa
Sadaukar da raina, a gare ka wannan karamin aiki ne

Zo kusantu dani, zana rayu dake
Amana ta kaina zana baki

Farin ciki na karuwa, idan na ganka a dama
So zai zama samu a rayuwa, tunda a kullum ina nema
Nayi godiya da dadawa, gun wanda shi ke ban dama
Bana yin nadama, haduwar mu ta hana inyo bakin ciki

Zo kusantu dani, zana rayu dake
Amana takaina zana baki
Zo kusantu dani, zana rayu dakai
Amana ta kaina zana baka