Rabo Dake

Rabo Dake

Umar M. Shareef

Альбом: Babbar Yarinya
Длительность: 4:02
Год: 2017
Скачать MP3

Текст песни

Bazan iya rabo dake ba
Mun saba da juna
Mi ye mafita a yanzu?
Ni bansan yadda za nayo ba

Bazan iya rabo da kai ba
Mun saba da juna (mun saba da juna)
Mi ye mafita a yanzu?
Ni bansan yadda za nayo ba

Na yarda dake mata ta baki bata raina
Dawainiya kinai min ba gajiya a dare da rana
Duk abinda nayi miki baki fushi ko ganin baki na
Halin ki akwai kyau, bazan so nayi rabo dake ba

Bazan iya rabo da kai ba
Mun saba da juna
Mi ye mafita a yanzu?
Ni bansan yadda za nayo ba

Duk wanda yayi ma ya cancanta gare shi ka nuna
Ka kula dani miji na ka nuna so da kauna
Komai na bida da hanzari ka faranta raina
Ban gano dalilin da zaya sa nayi rabo da kai ba

Bazan iya rabo dake ba
Mun saba da juna
Mi ye mafita a yanzu?
Ni bansan yadda za nayo ba

In har babu ke, rayuwa na rasa nishadi
So yana zaki, naki ya wuce zuma da madi
Mantawa da komai nake idan ki nai mini tadi
Bana iya barci, in ban gan ki a kusa dani ba

Bazan iya rabo da kai ba
Mun saba da juna
Mi ye mafita a yanzu?
Ni bansan yadda za nayo ba

Ina zubar hawaye a dalilin rashin ganin ka
Bukatu na a yanzu idanu suyi tozali da naka
Menene dalilin da yasa ake ta so na barka?
Koko rayuwa ce ba'a so nayi a duniya ba?

Mi ye mafita? Shi muke nema bamu daina ba
Yawan daga hannu muna ta roko gare ka sarki rabba
Kaji tausayin mu domin darajar annabin mu babba
Mu samu dai-daito a tsakanin mu bamu saba ba

Mun saba da juna
Mi ye mafita a yanzu?
Ni bansan yadda za nayo ba

Bazan iya rabo da kai ba
Mun saba da juna
Mun saba da juna