Abinda Ke Raina (Feat. Umar M Sharif)
Abdull D
3:29Hmmm, abokanai na taho da zance Zan baku labari a takaice Soyayya ance ruwan zuma ce Na dandana naji ruwan guba ce Nayi gamo wata yarinya ce Kyakkywa zuciya ta sace Na rasa ya zana yo kwatance In zana surar ta kar na mance Ta kai karshe gun kyau duniya ce Cikin yan mata ko fitila ce Ga dadin sauti Ta iya zance Kullum muna tare da maraice Idan nace mata amarya sai tace Kai kuma ango raina ta farance Na shirya aurenta koda da rance Don bani so wani ya mini kwace Kullum tunani in nayi kwance A daura auren mu kar na zauce Ashe cikin ranta babu zance Tasa abun sarkiya da kwance An sanya auren su kuji zance Mece dani kuce yaudara ce So in ya zamo cuta Ka dau hakuri shine magani Nima haka nan na fafata Soyayya ce ta koyar dani Kuji kadan labarin ta Halayya ce ta yan zamani Muna soyayya ni da ita Ta soni kamar ta shayar dani Dangi basu so na da ita Na nemi wa zai fahimtar dani Sun bincika halayyar ta Tasa niyya ta cutar dani Sun hada baki da zabin ta In an daura su kayar dani Sannan su kwashe dukiya ta Suyo aure su manta dani Nabi a sannu takun ta Na gane hakan ya rikitar dani A zuci ta sakan cuta Nai kuka da ido baji ba gani Gashi nai nutso cikin son ta Na dau hakuri ya warkar dani Naji zance ku na tausaya Amma kun sani fargaba Hakin da kuka shiga a soyayya Ni ko ban shige shi ba Ina da wacce muke tarayya Ta gaske mai ci gaba Ko bani lafiya zatai jinya Ba zata guje ni ba Ku dauki hakuri kuyo dace Ku sanya haka duk jarabta ce Kowa akwai nashi a rubuce Ba mai tsallake ta kaddara ce Wadansu kuka cikin duniya Wadansu sai dariya Mai hakuri tare yake da Allah Akwai ranar sakayya