Bazan Rayu
Umar M. Shareef
3:31Yaki a soyayya na shirya Taho mu buga yanmata Yanmata, ah-ah yanmata Yaki a soyayya na shirya Taho mu buga dan gata Dan gayu, ah-ah dan gata In kinka dau kibiya Ni kuma zani dau mashi Ba zana motsa ba Indai zaki harbo shi Zan sanya kirji na Ba tsoro in tarbe shi Cikin zuciyata ai nan ne masaukin shi Kinyo nasara a cikin yaki ki dauke shi Kin zamto sarauniya Duk mata kece dake gaba manufata Manufata ah-ah Gani in taso da gudu Na isko ka sai nishi Indai da soyayya Tabbas akwai kishi Kai daya zana ba rance Tunda kana biyan bashi Ka harbe ni Zana tsaya da harsashi Na soyayya baya kisa ko ya tashi Tun ranar daka sameni dashi jina nake wata autar mata Autar mata Sun koma da sun gan ki Kin masu kwarjini Sunyi bugu sun barki Kin sasu hawan jini Soyayyata ta taki Zo ki kula dani Indai na aure ki Baki guna-guni Naji giyar soyayya Kin shayar dani Nima dole in baki nawa Don kiyi masu rata Kiyi masu rata Haduwa ta da kai tayi riba Lokaci guda munka saba Ka zamo madubi na duba Abinda ka so inyi Zanyi shi ba aibu ba Aure na sanya a rai Da kai ka zamto uba Mu hado zuri'a da kai shine manufata Munufata Cikin su mazaje Kai ka zama auta na maza Cikin mataye Ai kecea autar mata Ra'ayi kuma riga Ke ki dau dankali ni gwaza A raina na sanyo ki Na baki kula yar gata Yar gata, ah-ah yar gata Dan gata, ah-ah dan gata Yaki a soyayya na shirya Taho mu buga yanmata Yanmata, ah-ah yanmata Yaki a soyayya na shirya Taho mu buga dan gata Dan gayu, ah-ah dan gata