Ranar Farin Ciki
Umar M. Shareef
4:40A gidan sarauta Sarauta, sarauta A gidan sarauta Dake zan daura aure Ki zamo sarauniya ta Kaine jarumi na Da kai zan daura aure Ina rokon Allahu Sarki Kare mu sharrin masu baki Yaye kunci ka bamu sauki Soyayyar mu ta kara zaki Hanya mun dauka Bama son sauka Zamu bi zabin ka Allahu komai kayi daidai Rabon ka naka ne bamai tsaidawa Hukuncin Rabbi shi ba mai sauyawa Komai ya iya, baya kasawa Komai na bar masa, sai nayi dacewa Yau murna ta Na zama mata Zanje nayi bauta na cika burina Da mafarkin ki nake kwana barci Da tunanin ki nake tashi barci Da kalaman ki suke kore kunci Daga kallon ki idanu ke sanyi Da mafarkin ka nake kwana bacci Da tunanin ka nake tashi bacci Da kalaman ka suke kore kunci Daga kallon ka idanu ke sanyi Na gamsu dake Na zabe ki ke Aure zanyi dake In saka ki a fada ta Lallai na tsallake Don an bani ke Na samu sake Zan nuna bajinta ta Tunda kika ce masu sai ni Ba zani saki kuka ba A kan ka bani jin kunya A ce na haukace a soyayya Samun irin ka kwai wuya, a'ah Wannan zamani duniya A kan ka zan yi komai In bada rayuwa ta Dake zan daura aure Ki zamo sarauniya ta Kaine jarumi na Da kai zan daura aure