Autar Mata

Autar Mata

Auta Waziri

Альбом: Autar Mata
Длительность: 4:20
Год: 2022
Скачать MP3

Текст песни

Auta Waziri kuke ji, malam

Kuzo kuji ga autar mata (beat Ali's production)
Karku taba mini yar gata
Kubar ni kawai nayi mata rawa
Babu irinta cikin mata

Kuzo kuji ga auta na maza
Karku taba mini dan gata
Kubar ni kawai nayi masa rawa
Babu irinsa cikin su maza

Autar mata (aah-ah)
Autar mata (ah-ah)
Autar mata
Kuzo kuji ga autar mata

Ko zaki na zuma baya ila
Naji tun farko
Bara na zube muku labari
Dana dan dauko
Dana tsunduma kogin soyayya
Nai ninkaya
Na hadu da 'ya mai alkunya
A daren farko

Mun shaku da ita a soyayya
Ba ja baya, abunda take so
Ta nuna kuma na dauko
Ku barni kawai ni nai nisa
Santa jikina yayai rasa
Babar magana wane bacci
A mafarkina naga mun aure

Kuzo kuji ga auta na maza
Karku taba mini dan gata
Kubar ni kawai nayi masa rawa
Babu irinsa cikin su maza

Autar mata (ah-ah)
Autar mata (ah-ah)
Autar mata
Kuzo kuji ga autar mata

Abunda nake so ka bani
Baka min karya
Gareni kazama cikon buri
Autar mata

Ka rike matakan soyayya
Kai baka zirya
To dole a saka a tarihi
Autar mata

A rai ka dasa mini soyayya
Kai daya ne da guri
Gareka nake dada tambihi
Autar mata

Gareni kazamto alheri
Da bai manta uwa
Abar ni dakai muyi soyayya
Kar miyo rabuwa

Kuzo kuji ga autar mata
Karku taba mini yar gata
Kubar ni kawai nayi mata rawa
Babu irinta cikin mata

Kuzo kuji ga auta na maza
Karku taba mini dan gata
Kubar ni kawai nayi masa rawa
Babu irinsa cikin su maza

Autar mata (aah-ah)
Autar mata (ah-ah)
Autar mata
Kuzo kuji ga autar mata

Sabo da maza akace jari
Nasan kin gano, ke zaki kure su a labari
Samun mace ince tamkar ki
Alkairi ne mah
Ki kauda dukan wani mai sharri

Kowa ya fada miki zai soki
Sam bai kawa ni
Haka in yake ba wani in kari
Na bar magana in ba hujja
So baya tabuwa
Mai yinsa yake masa linzami
Don kar ayai rabuwa

Kuzo kuji ga auta na maza
Karku taba mini dan gata
Kubar ni kawai nayi masa rawa
Babu irinsa cikin su maza

Autar mata (ah-ah)
Autar mata (ah-ah)
Autar mata
Kuzo kuji ga autar mata

Hmm, kace mini zamuyi soyayya
Tun haduwar farko
Amsa maka nayai ba jayaya
Autar mata

Kawayena sunyi mamaki
Yadda na dan sako
Ta yadda na amsa na shirya
Autar mata

Abun da yasa naji zan soka
Kayi zubin nutsuwa
Na bincika kyawun halaya
Autar mata

Bara na rufe maka labari
Sai da mukai shakuwa
Na gane ana gina soyayya
Har tai daduwa

Kuzo kuji ga autar mata
Karku taba mini yar gata
Kubar ni kawai nayi mata rawa
Babu irinta cikin mata

Kuzo kuji ga auta na maza
Karku taba mini dan gata
Kubar ni kawai nayi masa rawa
Babu irinsa cikin su maza

Autar mata (ah-ah)
Autar mata (ah-ah)
Autar mata
Kuzo kuji ga autar mata