Kina Nesa

Kina Nesa

Umar M. Shareef

Альбом: Ni Da Ke
Длительность: 3:24
Год: 2018
Скачать MP3

Текст песни

Ki na nesa da idaniya
Ki na kusa da zuciya

Kin yo nesa da idaniya ta
Ki na kusa da zuciya

Jigon rayuwa soyayya ce

Na taba jin hakan sai na mance
Da naga mai kuka asSo in ce kauce
Iya tunani na mai haka ya zauce

Yanzun gashi nan akan kai na, ina kuka kan Soyayya

Mun yiyo sabo da ke muna tare
Kullum in zo zance wurin ki in zanzare

Shaƙuwa ta kai Shakuwa aboki in karkare

Mun fara tunanin aure muja zare
Rashin ki yasa rana ya zam dare
Bana iya barci da idaniya

Duniya tayi daci
Rashin kine

Bana iya barci
Domin ki ne

Na zam a kadaici
Gani a jingine
Rayuwa ta kunci
Yayi kane-kane

Yaushe hawaye zai bar zuba, kzo ki tare aminiya

Yaya zan yi in misalta soyayya
Yaya zan yi in fasalta soyayya

Ita ce ba'a saye da kudi duk dukiya
Ita cemai gida na mulki shine zuciya
Ta sanya mai ƙarfi ya sunkuya

Ya zubda hawayen idaniya

Ki na nesa da idaniya
Ki na kusa da zuciya