Mikatin Rayuwata
Aminu Alan Waka
Tafiya ta, nakusa kai wa Kwanakina, suna wucewa Cikin jakata, ban sani ba Guzirina, tayaya zan iske gida Buri na raina shine in sai gidaje Daki na kwana,in sa gadaje Motar hawana, duk inda zanje Ana rakona, comboy kamar kudaje Inata fankama, inata cije-cije In canza kaya, kullum in gyara saje Bana tunawa, da inda nai fitowa Namanta cewa, watarana zan komawa Na cinye komai, bani tattalawa Koda sakoma, bani turawa Na yanki visa, ta kusa karkarewa Kuma babu dama, bare inyo dadawa Wayyo ni, wayyo Wayyo ni, wayyo Wayyo ni, wayyo Ya zanayo dakaina Akwai gida nabiyu inda zani kwanta Gidan da ba'a zama ciki da mata Babu iyaya 'ya'ya bare makwabta Abinda nazo, dashi zani zanta Abinda ni na rubuta shi zan karanta Bawanda zaya aje bare na sata In nayi kirki, ba mai yi man mugunta Wayyo ni, wayyo Wayyo ni, wayyo Wayyo ni, wayyo Ya zanayo dakaina Allah yaso ni, tunda na ankare Sai in kara kaimin nema, cikin darare In ci lokacina, kafin ya karkare Abinda nasamu, sai in tattali In aika gida, in naje mu warware Gida na ukku, in da ba'a boye-boye Duk wanda ya mutu, rannan ka ganshi raye Kowa a girme, ba wanda ke a goye Wasu suyita murna, wasu suyi zubar hawaye Abinda ka aika, shi zaka sama Mu aika alkhairi, muje mu sama