Barauniya

Barauniya

Umar M. Shareef

Альбом: Ni Da Ke
Длительность: 3:34
Год: 2018
Скачать MP3

Текст песни

Na gamu da barawniya tai mini sata
Tayi tafiya ina nemanta
Ina ta cigiya wa ne ya ganta
Abokanai na ko kun san gidan ta
Waye zai fada min in mi shi kyauta
Ku taimaka min karna wahalta
In je in ne mo kar na salwanta. haaaaaaa lalalaaaa
Barawniya haaaaaa
Aaa

Ta sace zuciya ta
Wayyo ta mallaketa
Ta sa ina ta san ta
Dube ni na jigata
Zan so ta bani nata
In je in mallaketa
Da zata ji abunda na keji a cikin zuciya
Da ba ko shakka ni na san sai ta tausaya kar da na yo jinya
Kin ba ni soyayya
Sani akan hanya ki je da niiiii hiii

Ta tafi da ni tuni zuciya ta ta dauka
Baji ba gani an kira ni mai hauka
Ko a studio ban iya waka
Zance ana tayi bana dauka
Son ta ya shige jiki ya narka
Wani lokaci sai in saka kuka
Ta kan yi min gizo
Ta ce da ni in zo

Da na iso ta shige cikin hazo
Banganta ba
Banganta ba
Bangata ba

Abokanai sun kace in hakura
Naki jin su ina faman jira
Tako ina cigiya ina bara
Akarshe sai na dauki shawara
Na karkare zani hakura
Watarana ina yin tafiyata

Ni da Dino ya kaimu a mota ta
Za muje restaurant mu rage ta
Bayan mun isa kwatsan na ganta
Ta na cin abinci da jarumin ta
Ashe mijin ta ne ashe mijin ta ne ashe mijin ta neh heye