Yaushe Zaki Dawo
Umar M. Shareef
3:41(Rub Master) Idan na rasa ki baza na ji dadi ba Idan na rasa ka baza nayi aure ba In na rasa ki baza na ji dadi ba Soyayya jigon rayuwa ta Nima in na rasa ka baza nayi aure ba Soyayya jigon rayuwa ta Zo na baki guri zauna Babu kamar ki a kalbi na Ke zan nuna wa dangi na In fada masu nayi mata Tuntuni na gama tari na Na zo gurin ki mu tattauna Batun auren mu muradina Tunda dai mun daidaita In na rasa ki baza nayi aure ba Don kece warakar damuwa ta Ni, na yarda na zam mai daki A gidan inyi maka aiki Aure indai da sadaki an gama komai Kai zaka zamo mai mulki In hada maka rigar saki Ka saka ta ka hau kan doki Ka zama jarmai Indai da akwai ka basa mini komai ba Don kaine ka zamo garkuwa ta In na rasa ki baza na ji dadi ba In na rasa ka baza nayi aure ba Soyayya jigon rayuwa ta Soyayya jigon rayuwa Na hango ki a sahun gaba Cikin matan kece gaba Dukan sauran basu kai ki ba Sun biki a baya Su duka da yan uba Ke suka martaba Kin zama jagaba Suka ce basu hangi kamar ki ba Ko manyan basu fiki da komai ba Shiyasa na kira ki da yar autar mata Zan hau in ka yarda Doki na kara danda Da gudu in shigo fada In fadi cikin wasa Siyan nagari kudi a gida Mai kyau baya yimin tsada Ayiri-yiri ranar murna Kyautar kaina na bada Bazan so a saka shi da nisa ba Ranar auren mu da kai ya kinmata In na rasa ki ina zan kwana, masoyiya? In na rasa ka a daina batu na, an rufe babi na Wanda yaso jin labari na, yazo gun ki ya zauna Babu abinda ya boyu a kaina, kasan duka sirri na Tun haduwar mu ba kiyi mini karya ba Ai tun haduwar mu ba kayi mini karya ba masoyi na