Hisabi
Umar M. Shareef
3:41Meera-Meera (ahh-aha) Meera-Meera (ahh-aha) Meera-Meerah (ahh-ahh) Kin shiga zuciya da raina Meera Bani zuma ta so in sha don wakar ki zanyi yanzu Kai na saka a zuciyata Meera Amshi zuma ta so kasha muyi waka yanzu-yanzu Bani zuma in sha kyauta ta masoya Za ta saka in kara zaki daga murya In nayi baituka da kyau ke kika sanya Za na yabe ki gimbiya ke sanadin farin ciki na Za na yabe ka saurayi kai ne farin ciki na Kin shiga zuciya da raina Meera Bani zuma ta so in sha don wakar ki zanyi yanzu Ka shiga zuciya kuryar ta ka kwanta A gadon ka na karbi kaunar ka wacca kauna ta kafata Ko guduma da bindiga basu cire ta Kai sha'anin ka saurayi watarana kai miji na Kiyi sha'anin ki yar budurwa kece farin cikina Kai na saka a zuciyata Meera Amshi zuma ta so sha muyi waka yanzu-yanzu Bana ruwan ido Meera a so ke na zaba Dai-dai da gwargwado za na kula ki babu kwaba Muje filin cido za na tsaya bazan guje ba Sai nayi hubba ko ban iya ba Jarumta ta zana nuna koda zan rasa raina Jarumta ta zana nuna saboda so da kauna Kin shiga zuciya da raina Meera Bani zuma ta so in sha don wakar ki zanyi yanzu Ado na tafiya waiwaye kai na waiga Duba ina ta yin zagaye nayi yanga Wankan da nayi ba jirwaye na saka riga Idan na samu gu nayi shiru kai nake tunawa Idan na samu gu nayi shiru ke nake tunana Na tausaya wa mai yin so da ba'a son shi Kalma take da zafi kama da rushi Ko a baki dadi soyayya ambata shi Zo ki fada da kanki dadi zai zo kunnuwa na Zana fadi kayi murna jindadin idanuwana Kin shiga zuciya da rai na Meera Bani zuma ta so in sha don wakar ki zanyi yanzu Kai na saka a zuciyata Meera Amshi zuma ta so kasha muyi waka yanzu-yanzu